Take a fresh look at your lifestyle.

Kafofin Watsa Labarai Zasu Anfana Daga Musayar Kudi Ta Naurar Zamani

251

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Muhammed Idris, ya bayyana aniyar gwamnati na samar da kayan aiki na Naurarr zamani ga hukumar yada labarai ta Najeriya.

 

Wannan sanarwar ta fito ne a yayin wata ziyarar ban girma da jami’an hukumar yada labarai ta Najeriya BON suka kai a Abuja.

 

Alhaji Idris ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci bankin masana’antu da ya saukaka wannan shiri, da nufin tallafawa da inganta harkar yada labarai a kasar nan.

 

“Ministan kasuwanci da masana’antu ya samu umarni domin tabbatar da samun saukin gudanar da lamuni idan ya dace,” in ji Alhaji Idris.

Yayin da yake jaddada kudirin gwamnati na magance kalubale a cikin masana’antar watsa shirye-shirye da kuma daidaitawa tare da mafi kyawun ayyuka na duniya, Ministan ya bayyana sadaukarwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaban fannin ta hanyar ba da tallafin kudi mai mahimmanci domin shawo kan kalubalen tattalin arziki na yanzu.

 

Bugu da kari, Ministan ya bayyana aniyar gwamnati na hada kai da wasu kafafen yada labarai masu zaman kansu domin samar da yanayi mai inganci na gudanar da harkokin kasuwanci a kasar.

 

Darakta Janar na NTA Alhaji Abdulhameed Dembos da sabon shugaban kungiyar sun mika godiya ga kokarin gwamnati na shigar da kafafen yada labarai.

 

Ya kuma yi kira da a mayar da kafafen yada labarai daga hukumar NCC zuwa hukumar da ta dace domin daidaita ayyukan.

 

Dembos, ya ba da shawarar kara yin hadin gwiwa da gwamnati, ya bukaci a yi nazari mai zurfi kan tsarin tantance masana’antar watsa labaru, yana mai jaddada wajabcin samar da kudaden da ake bukata domin gudanar da aiyyuka.

Ziyarar gaisuwar ta hada da halartar manyan daraktoci, Mallam Jibrin Baba Ndace na Muryar Najeriya VON, Dr. Mohammed Bulama na FRCN, da Mista Charles Ebuebu na hukumar yada labarai ta kasa NBC.

 

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.