Kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya na iya fitar da matakan gaggawa da ke ba Isra’ila umarnin dakatar da ayyukan soji a Gaza.
Zaman kotun kasa da kasa ta ICJ a yau Juma’a wani bangare ne na shari’ar da kasar Afirka ta Kudu ta gabatar na zargin Isra’ila na aikata kisan kiyashi.
Kasashen biyu sun ba da shaida lokacin da aka bude shari’ar makonni biyu da suka gabata. Isra’ila ta yi watsi da zargin.
Hukuncin da aka yanke wa Isra’ila ba kotu ba ce za ta aiwatar da shi amma zai kasance mai mahimmanci a siyasance.
Fiye da Falasdinawa 25,000 akasari mata da yara ne aka kashe tare da jikkata dubunnan dubbai, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, tun bayan da Isra’ila ta fara kai hare-hare, sakamakon harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kasar Afirka ta Kudu mai matukar goyon bayan Falasdinawa, ta bukaci kotun da ta fitar da wasu matakai na wucin gadi guda tara da suka hada da dakatar da ayyukan soji da Isra’ila ke yi, yayin da take la’akari da zargin kisan kare dangi. Ba a tsammanin yanke hukunci a kan na ƙarshe na dogon lokaci, watakila shekaru.
Isra’ila ta mayar da martani da bacin rai game da zargin kisan kare dangi, inda ta zargi Afirka ta Kudu da karkatar da gaskiya. Ta ce tana da hakki ta kare kanta kuma tana kai wa mayakan Hamas hari, ba farar hula Falasdinawa ba.
BBC/Ladan Nasidi.