Ministocin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun halarci taron “Komawa Gaza” don tsara matsugunan da ba bisa ka’ida ba a kan al’ummar Palasdinawa da aka lalata kwanan nan.
Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan Khan Younis yayin da aka tilasta wa Falasdinawa da yawa zuwa Rafah mai cike da hadari a kudancin Gaza.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana sabon tattaunawar da aka yi kan musayar fursunoni a matsayin “mai amfani”, amma ya ce akwai gibi.
Akalla mutane 26,422 ne suka mutu yayin da wasu 65,087 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba. Adadin wadanda suka mutu a Isra’ila sakamakon harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 1,139.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.