Firayim Ministan Habasha ya ce jirgin farko da aka gina a Habasha a 1935 Italiya ta mayar da shi kasar.
An ɗauke shi a lokacin mulkin Fasistiyawa na Italiya a lokacin mamayar abin da yake a lokacin Abyssinia, a ƙarshe an nuna shi a gidan kayan tarihi na jiragen sama na Italiya a Roma.
An ba da shi ga Firayim Minista Aby Ahmed a hukumance a wani biki a Rome kuma ya ce wannan rana ce ta “ranar alfahari” ga kasar.
Jirgin da aka fi sani da Tsehai, an ce an sanya wa jirgin sunan ’yar Sarki Haile Selassie a lokacin.
BBC/Ladan Nasidi.