Take a fresh look at your lifestyle.

PDP Ta Nada Toyese A Matsayin Mataimakin Shugaban Kudu Maso Yamma

82

Kwamitin ayyuka na kasa, NWC na jam’iyyar PDP, ya amince da nada Mista Ajisafe Toyese daga jihar Osun a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a yankin Kudu maso Yamma.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Mista Debo Ologunagba a Abuja.

 

A cewarsa, amincewar nadin Toyese ya samu amincewar kwamitin ayyuka na jam’iyyar a madadin kwamitin zartarwa na kasa, NEC.

 

Ya kara da cewa nadin Toyose ya biyo bayan rasuwar tsohon mataimakin shugaban shiyyar, Mista Soji Adagunodo, wanda ya rasu a ranar 20 ga Mayu, 2023.

 

“An amince da nadin ne a taron da aka yi kwanan nan na shiyyar Kudu maso Yamma na jam’iyyar bisa tanadin sashe na 46 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar kamar yadda aka yi wa gyara a shekarar 2017,” inji shi.

 

Jam’iyyar ta bayyana Toyese a matsayin dan jam’iyya mai biyayya wanda ya yi wa PDP hidima a matsayin dan majalisar yakin neman zaben shugaban kasa a 2023.

 

“Lauya ne kuma Injiniya wanda kuma ya taba zama Mataimakin Darakta Janar na Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP na 2023,” in ji shi.

 

“Jam’iyyar PDP tana alfahari da jajircewar Toyese wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban jam’iyyar da kuma samun nasarar jam’iyyar, musamman wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na hada kai ga jam’iyyar a matakai daban-daban.

 

“Ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna Ademola Adeleke, mataimakin darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa baya ga wasu muhimman ayyuka da suka hada da zama wakilai na kasa a taron PDP.

 

“Muna rokonsa da ya yi amfani da sabon matsayinsa don kara hada kan jam’iyyar, zage-zage da kuma karfafa jam’iyyar a shiyyar tare da yin aiki tare da sauran shugabannin don ci gaba da samun nasarar jam’iyyar,” Ologunagba ya kara da cewa.

 

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

Comments are closed.