Fadar shugaban kasa ta Najeriya ta ce ba ta amince wa wata jiha ta kasa ta mallaki makamai masu sarrafa kansu ba don jami’an tsaronta.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha fadin cewa babu wani dan kasa ko jiha da za a bari ya siyo AK 47 ko wani makami ba bisa ka’ida ba.
A cewar Shehu: “Fadar shugaban kasa na son tabbatar da cewa babu wata jiha, ba Katsina ba, babu wata jiha a cikin tarayya da aka ba su izinin sayo makamai masu sarrafa kansu na kayan tsaro.
“A karkashin wannan gwamnatin, shugaban kasar ya sha bayyana karara cewa babu wanda aka yarda ya dauki AK-47 ko wani makami ba bisa ka’ida ba kuma idan yana da irin wadannan makaman to dole ne ya mika shi.
“A inda suka kasa yin hakan, an baiwa jami’an tsaro kwakkwaran umarni don tunkarar duk wani mai irin wannan doka.
“A karkashin dokokin da ake da su, ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa ne kadai zai iya bayar da irin wannan izini, bayan da shugaban kasa da babban kwamandan su suka ba da izini.
“Kamar yadda yake a halin yanzu, ba a ba wa kowace gwamnati irin wannan amincewar ba.”
Ya bayyana musamman yadda jihar Katsina ta kasance, inda mutane da yawa ke ganin ta samu makamai.
“A jihar Katsina sau da yawa ana ambato Gwamna Aminu Bello Masari ya rubuta cewa gwamnatin ta gayyaci Shugaban Kwalejin horas da jami’an tsaro ta Civil Defence da ke Katsina domin horar da ‘yan banga na tsawon kwanaki biyar a kan yadda ake sarrafa da kuma gudanar da ayyukan Bindigar Pump Action Rifles. ,’ tare da jaddada cewa ba a horas da ‘yan banga don karbar ayyukan hukumomin tsaro na gwamnatin tarayyar Najeriya sai dai don taimaka musu.
“Fadar shugaban kasa ta yaba da yadda jihohi ke sa baki a harkokin tsaro.
“Musamman shugaban kasar ya bayyana farin cikinsa cewa a cikin shekaru biyun da suka gabata, an alakanta kayyakin tsaro da gwamnatocin jihohi ke da shi da wasu muhimman tsare-tsare, kuma rahotanni sun zo masa na bajinta da kwarewa.
“Duk da haka, ya yi gargadi game da siyasantar da tsaro”.
Leave a Reply