Shugaban gungun kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa shirye-shiryen gwamnati don ganin an tallafa wa al’umma da ke fama da matsaloli na tattalin arziki a jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya.
Dangote ya bayyana haka ne yayin ganawa da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatin Kano a wannan rana ta Juma’a. Matakin da ke zuwa yayin da al’umma ke ci gaba da fama da kakanakayi saboda yadda farashin kayan masarufi yayi tashin gorin zabi a fadin kasar.
A wasika dauke da sa hannun daraktan yada labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa yace Dangote kai tsaye yayi alkawarin talafa wa jihar ta Kano a fannoni na lafiya da ilimi da tallafa wa marasa karfi da ke fama da kakanakayi a rayuwa.
“Mun zo nan don mu taya murna ga gwamnan Kano saboda nasarar da ya samu a kotun koli, ina ba ka tabbaci na baka goyon baya a tsawon wa’adin mulkinka wanda ba lallai bane shekaru hudu ba, shekaru talkwas. ”
“Ko da dai mai gabatarwa ya bayyanani a matsayin bakar fata mafi kudi a Afurka amma kana iya bayyanani a matsayin Bakano, ni mai biyayya ne da a ko da yaushe za a iya neman hadin kai na a hanyoyin da za a ciyar da Kano gaba.”
“Don cimma wannan manufa dole mu duba yadda za a samar da ci gaba a bangaren lafiya da ilimi da tallafa wa al’umma, ya za mu tallafa wa gwamnati saboda gwamnati ita kadai ba za ta iya ba.”
A nasa bangaren gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci tallafin hamshin mai kudin don ya tallafa a samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta a jihar ta Kano ta yadda za a farfado da masana’antun jihar da ke da tarin matsaloli, tattalin arzikin jihar ya bunkasa.
Har-ila-yau gwamnan ya fada wa Dangote cewa jihar na matukar bukatar a samar da asibiti na masu cutar sikila ta yadda za a rika basu magani kyauta. Ya kuma bukaci ya kammala manyan ayyuka da ya faro karkashin Gidauniyar Dangote a asibitin Murtala da ke jihar ta Kano.
Yusuf Bala.