Take a fresh look at your lifestyle.

Amurka Ta Ce Muhimmin Garuruwan Ukrain Zai Iya Fadawa Hannun Rasha

80

Amurka ta yi gargadin cewa Rasha za ta iya kwace muhimmin garin Avdiivka na gabashin Ukraine, wurin da aka gwabza kazamin fada a ‘yan watannin nan.

 

Kakakin kwamitin tsaron kasar John Kirby ya ce, “Avdiivka na cikin hadarin fadawa hannun Rasha.”

 

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya sha alwashin yin duk abin da zai “ceci rayukan ‘yan Ukraine da yawa kamar yadda zai yiwu”.

 

Dakarun Rasha sun samu galaba a Avdiivka, inda suka yi barazanar kewaye shi.

 

Garin da ya kusan rugujewa ana kallonsa a matsayin wata hanyar zuwa Donetsk da ke kusa, babban birnin Yukren da mayakan da ke samun goyon bayan Rasha suka kwace a shekara ta 2014 sannan kuma Masko ta mamaye ta ba bisa ka’ida ba.

 

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kaddamar da wani gagarumin farmaki kan kasar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022.

 

A wani taron tattaunawa da aka yi a Washington, Kirby ya ce Avdiivka na iya faduwa sosai “kayan yakin Yukren na manyan bindidgogi da Albarusai na  sojojin kasa suna karewa “.

 

“Rasha na aika da guguwar soji don kai hari kan wuraren Yukren,” in ji shi.

 

“Kuma saboda har yanzu Majalisa ba ta zartar da karin kudirin ba, ba mu iya ba wa Yukren makaman atilare da suke matukar bukata don dakile wadannan hare-haren na Rasha ba.

 

Yanzu haka sojojin Rasha sun isa ramukan Ukraine a Avdiivka, kuma sun fara mamaye tsaron Yukren.”

 

Yukren ta dogara sosai kan samar da makamai daga Amurka da sauran kawayenta na Yamma don samun damar ci gaba da yakar Rasha – rundunar soji mafi girma da tarin alburusai.

 

Sakatare Janar na Nato Jen Stoltenberg ya yi gargadin cewa gazawar Amurka na amincewa da ci gaba da taimakon sojojin Yukren zai kawo koma bayan dakarun Yukren a fagen fama.

 

 

 

BBC/Ladan Nasidi.

Comments are closed.