Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Ya Isa Addis Ababa Domin Halartar Taron AU Karo Na 37

241

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha domin halartar babban taron kungiyar Tarayyar Afirka karo na 37.

 

Shugaban zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka wajen gudanar da manyan tarurruka kan sauye-sauyen hukumomin Tarayyar Afirka; zaman lafiya da tsaro; musamman batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, da kuma hanyoyin shiga da kuma abubuwan da suka sa a gaba a kungiyar ta G20.

 

Karanta Haka: Shugaba Tinubu Zai Halarci Taron AU Na 37 A Addis Ababa

 

Har ila yau, shugaba Tinubu zai halarci wani babban taro na musamman na hukumar shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS a matsayinsa na shugaban kungiyar na yankin.

Taken taron kolin na bana shi ne ”Kwatar da wani dan Afirka da ya dace da karni na 21: Gina tsarin ilimi mai juriya don kara samun dama ga ci gaban ilimi, tsawon rai, inganci, da kuma dacewa da koyo a Afirka”.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.