Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Nada Hafsat Bakare Sabuwar Shugabar Hukumar NFIU

218

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Ms. Hafsat Abubakar Bakare a matsayin Darakta kuma Babbar Jami’ar Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NFIU), har sai Majalisar Dattawa ta tabbatar da ita.

 

An bayyana nadin Bakare ne a ranar Talata a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale.

 

Kafin a nada ta a matsayin babbar jami’ar NFIU, Bakare ta kasance mataimakiyar darakta a sashin kula da harkokin kudi na Najeriya, kuma a lokuta daban-daban ta kasance shugabar sashen kula da ayyukan gwamnati; Shugaban Sashen Dabaru da Sakewa, kuma Shugabar Sakatariyar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).

 

Ms. Bakare lauya ce kuma ƙwararriyar mai leƙen asiri ta kuɗi ce tare da gogewar shekaru masu yawa a yaƙi da haramtattun kudaden da ake tallafa wa ayyukan ta’addanci (AML/CFT/CPF).

 

Shugaban kasar na fatan Malama Bakare zata kawo kwarewa da gogewa domin samun cikakkiyar nasara a sabon aikin nata, musamman ganin yakin da gwamnatin Tinubu ke yi da haramtattun kudade.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.