Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yakin da aka kwashe watanni 10 ana gwabzawa a kasar Sudan na nufin rashin abinci mai gina jiki na kara ta’azzara a yankin kuma yana haifar da rikicin kabilanci mafi girma a duniya.
Akalla mutane miliyan 25 ne ke kokawa da karuwar yunwa da rashin abinci mai gina jiki yayin da rikicin Sudan ya jefa fargaba a yankin, kamar yadda hukumar ta sanar.
WFP ta kuma nuna rashin jin dadin yadda ake fama da karancin kayan aiki da nufin magance matsalar jin kai.
“A halin yanzu abin takaici muna da kuɗi kuma ba mu da damar isa ga mutane a cikin buƙatun da ake da su yanzu.”
Dubban iyalai ne ake gudun hijira tare da tilasta musu tsallakawa kan iyakokin kasashen Chadi da Sudan ta Kudu a kowane mako, in ji Annabel Symington, mai magana da yawun WFP.
Kimanin mutane miliyan 1.8 da suka tsere daga yakin galibi sun sami mafaka a makwabciyar ta Chadi da Sudan ta Kudu amma wadannan suna kokawa da nasu rauni.
“A cikin wadannan kasashen biyu damina na zuwa nan ba da dadewa ba kuma da hakan zai kara wahala wajen isa ga mutane. Muna buƙatar yin taimako a yanzu domin tabbatar da cewa za mu iya ci gaba da mayar da martani. Ba za mu iya yin hakan ba, Saboda yankin Chadi, Sudan ta Kudu, suna fama da matsalar yunwa. Saboda haka wannan shine ainihin rikicin ”.
A Sudan ta Kudu, iyalai da ke gudun hijira a Sudan yanzu su ne kashi 35% na wadanda ke fuskantar bala’in yunwa, duk da kashi 3% na al’ummar kasar.
Adadin rashin abinci mai gina jiki yana ƙaruwa cikin sauri a tsakanin yaran da ke cikin wahala a sansanonin wucewa na wucin gadi, kamar sansanin a Renk.
A cewar WFP, kusan kashi 4 cikin 100 na yara ‘yan kasa da shekaru 5 da ke tsallaka kan iyaka zuwa Sudan ta Kudu na fama da rashin abinci mai gina jiki yayin shiga kasar.
Kimanin mutane miliyan 18 ne ke fama da matsalar karancin abinci a Sudan sannan kuma kimanin yara miliyan 3.8 na Sudan ‘yan kasa da shekaru 5 na fama da tamowa, a cewar WFP.
Sai dai wadanda ke tsallaka kan iyaka zuwa Sudan ta Kudu suna hade da iyalai wadanda tuni keda karancin abinci da matsananciyar yunwa.
Yaki na shekaru biyar da ambaliya da ba a taba ganin irinsa ba ya jefa Sudan ta Kudu kanta cikin wani mawuyacin hali inda sama da kashi 75% na al’ummar kasar miliyan 12 ke bukatar agajin jin kai, yayin da kusan miliyan uku ke fama da yunwa.
Africanews/Ladan Nasidi.