Anambra Civil Society Network (ACSONET), wata dandali na masu ruwa da tsaki na Jama’a, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya game da hari da kashe sojoji da suke sintiri na yau da kullum a Umunze, karamar hukumar Orumba ta Kudu a jihar Anambra, wanda har yanzu ba a tantance wadanda suka kai harin ba.
A cikin wata sanarwa da shugaban ACSONET, Prince Chris Azor ya fitar, “Muna yin Allah wadai da wannan mummunan aiki da rashin tsoro, kuma muna bukatar hukumomi su sa baki cikin gaggawa don tabbatar da kama masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.
Azor ya roki gwamnati a matakin kasa da na Jihohi da ta kara sanya ido da kuma matakan tsaro don tabbatar da isasshen kariya na rayuka da dukiyoyi.
“Yayin da muke shiga yakin neman zabe na siyasa don zaben kasa mai zuwa, dole ne jami’an tsaron mu su nuna a shirye suke domin kare rayukan ‘yan kasa. Idan ba a manta ba a baya-bayan nan ne aka kaiwa ayarin motocin Sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, Cif Ifeanyi Ubah hari, inda aka kashe mutane da dama. Wannan sam ba za a yarda da shi ba” ya kammala.
Don haka mai fafutukar kare hakkin bil’adama, ya bukaci ‘yan kasar da su yi amfani da dokar da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su, ta hanyar taimaka wa hukumomi a kodayaushe wajen dakile miyagun laifuffuka ta hanyar ba da bayanai masu amfani cikin gaggawa da kuma hada kai da hukumomi bisa doka.
Leave a Reply