Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu A Doha Domin Ziyarar Taimako

57

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Doha domin gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki biyu da nufin karfafa huldar da ke tsakanin kasashen biyu, da inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Qatar a fannin tsaro, musanyar al’adu, da bunkasar tattalin arziki.

 

Shugaban wanda ya isa kasar Qatar da karfe 23:25 na yammacin ranar Alhamis, ya samu tarba daga ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ministan kudi, Mista Wale Edun, ministan lafiya Ali Pate da gwamnan jihar Kaduna, Sani Uba.

 

Haka kuma a filin jirgin saman Doha domin tarbar shugaban na Najeriya akwai manyan jami’an gwamnatin kasar Qatar.

 

Shugaba Tinubu ya karrama goron gayyata da mai martaba, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, Sarkin Qatar, ya yi masa, domin ya shaida rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin da suka mayar da hankali wajen bunkasa fagagen Najeriya na hakika da kuma samar da jari mai amfani a fannonin kasuwanci. ilimi, ma’adanai masu ƙarfi, tattalin arziƙin dijital, noma, da iskar gas, tare da haɓaka haɗin gwiwa kan yaƙi da ta’addanci.

 

A yayin ziyarar, shugaba Tinubu zai kuma halarci wani taron kasuwanci da zuba jari wanda zai hada manyan jami’ai a sassa masu zaman kansu da na gwamnati na Najeriya da Qatar don ciyar da damammaki daban-daban na ci gaba da ci gaban juna.

 

Shugaban ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati.

 

 

Ladan Nasidi

Comments are closed.