Shugaba Bola Tinubu ya amince da cikakken kundin tsarin mulkin tawagar gudanarwa na Kamfanin samar da wutar lantarki mallakar Gwamnatin Tarayya, tare da sake nada Kenny Osebi Anuwe a matsayin Manajan Darakta da Babban Jami’in Gudanarwa.
Shugaban ya kuma sake nada Farfesa Mamman Lawal a matsayin sakataren kamfanin kuma mashawarcin shari’a na kamfanin.
An bayyana wadannan ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu.
Wadanda aka nada don yin aiki na sabon wa’adin sune Ebenezer Olawale Fapohunda, Babban Jami’in Fasaha; Babatunde Daramola Oniru, babban jami’in kasuwanci; da Julius Oyekola Olabiyi, babban jami’in kudi.
Shugaba Tinubu ya dorawa tawagar gudanarwar kamfanin samar da wutar lantarki ta FGN aiki tukuru don ganin an cimma manufofin shirin samar da wutar lantarki na shugaban kasa (PPI) tare da hadin gwiwa da kamfanin Siemens Energy ta hanyar fadada hanyar sadarwa ta kasa.
Ladan Nasidi.