Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Injiniya Oluwagbenga Ajiboye a matsayin Babban Darakta na Kamfanin Sadarwa na Najeriya, TCN.
President Bola Ahmed Tinubu appoints four Nigerian professionals as Executive Directors of TCN:
1. Engineer Oluwagbenga E.A. Ajiboye – Executive Director, Transmission Service Provider
2. Engineer Nafisatu Asabe Ali – Executive Director, Independent System Operations
3. Ochije… pic.twitter.com/Co14Q9RYdg
— Voice of Nigeria (@voiceofnigeria) March 1, 2024
Shugaban ya kuma nada Injiniya Nafisatu Asabe Ali a matsayin babban darakta mai kula da ayyuka masu zaman kansu, Ochije Ogini Chukwuka a matsayin babban daraktan kudi da asusu da kuma Abiodun Foluso Afolabi a matsayin babban darakta na ma’aikata da ayyukan kamfanoni.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa kwararrun za su yi wa’adin shekaru hudu ne da za a sabunta su.
Ladan Nasidi.