Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar Da Ayyukan Cigaba Ga Al’umma 74 A Jihar

Kamilu Lawal,Katsina.

316

Hukumar inganta rayuwar al’umma ta jihar Katsina CSDA ta kaddamar da ayyukan al’umma na Naira Miliyan dari takwas da tamanin da takwas (₦:888,000,000) da za’a gudanar ga al’umma 74 (74 Communities) a fadin jihar Katsina.

 

Ayyukan da hukumar zata gudanar ga wadannan al’ummomi wato (Communities) sun hada da gina azuzuwa ko gyarawa, gina asibiti ko gyarawa, magudanun ruwa ko gyarawa, gina sabbin rijiyoyin burtsatse ko gyarawa da dai sauran su.

 

Hukumar ta kaddamar da bada horo gami ba bada takardar karba kudi (Check) kashi na farko ga wasu al’ummomin kananan hukumomin Daura da Baure da Ingawa da Mai’aduwa da kuma Kusada da zasu amfana da wannan aiki.

 

Da yake gabatar da jawabin sa shugaban hukumar ta CSDA Alh. Dikko Abdulaziz ya bayyana cewa ” muna godiya ga Allah da ya kawo mu wannan rana wadda muka zo domin kaddamar da fara aikin mu na wannan shekara ta 2024 a Daura, inda al’ummomi 74 ne zasu amfana dashi a fadin jihar Katsina, wanda a yau mun kaddamar da kashi na farko na rabin wannan al’ummomi.

 

Wanda bayan sati biyu zamu dawo domin kaddamar da kashi na biyu da sauran al’ummomin da suma zasu amfana. Daga karshe muna mika cikakkar godiyarmu ga gwamnan jihar Katsina Mal. Dikko Umar Radda bisa irin gudunmuwa da taimako da yake ba wannan hukuma.

 

Shima a nasa jawabin manajan ayyuka na hukumar Alh. Lawal Suleiman Riko yayi jawabi mai tsawo a kan ka’idojin aikin. Shima Manajan Kudi na Hukumar, Alh. Magaji Yusuf Bakori ya bayyana yadda tsarin bada kudin yake inda yace yanzu za’a bada kaso hamsin ne na kudin wanda bayan cika dukkan ka’idojin aikin za’a cika sauran kudin.

 

Daga karshe ya bada shawarwari na yin duk abinda ya dace wajen gudanar da wannan ayyuka gami da cika dukkan ka’idojin da aka cika na wannan aiki wanda sune zasu gudanar da kansu ba dan kwangila ba.

 

Shima a nasa jawabin na godiya shugaban karamar hukumar Daura wanda ya samu wakilcin sakataran sa Hon Iliyasu Madobi ya yaba ma hukumar ta CSDA bisa yadda suke gudanar da ayyukan su a fadin jihar Katsina.

 

Daga karshe ya mika cikkar godiya ga gwamnan jihar Katsina Mal Dikko Umar Radda bisa yadda yake kokarin  wajen tallafa ma irin wadannan hukumomi dake taba rayuwar al’umma kai tsaye.

 

Jami’an hukumar da dama ne suka gabatar da jawabai, kasida gami da lakcoci ta yadda ake gudanar da ayyukan hukumar wanda suka hada da Haj. Maryam Liadi da Dr. Samaila Balarabe da Rumassa’u Abdullahi.

 

Akwai kuma Ahmad Rabiu Kankia da Aminu Hassan Gafai da Engr. Abbas Sulaiman da Ibrahim Umar da kuma Habiba Abubakar. Bayan kamalla taron an bada dama ga mahalarta taron domin yin tambayoyi gami da mika masu takardun kudin nan take.

 

Kamilu Lawal.

Comments are closed.