Matasan jihar Katsina na cikin farin ciki a yayin da suke jiran isowar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a jihar a yau Asabar.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai kaddamar da wani shiri na karfafawa wanda babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin siyasa Alhaji Ibrahim Masari ya dauki nauyi.
Kayayyakin da za a raba sun hada da kekunan dinki da walda, babura, bas da motoci da dai sauransu.
Mai taimaka wa shugaban kasar na kallon wannan karimcin a matsayin ‘yar hanyarsa na taimakawa wajen dakile illolin koma bayan tattalin arzikin da ake ciki a yanzu.
Tuni dai an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen wurin da aka gudanar da bikin a karamar hukumar Kafur.
Ladan Nasidi.