Take a fresh look at your lifestyle.

Matsalilin Ciwon Yoyon Fitsari da Mata Ke Fama da su a Nigeria: Ina Mafita?

Shehu Salman, Sokoto.

130

Ciwon yoyon fitsari matsala ce da mata musamman marasa karfi ke fama da shi a Nigeria.

A daidai wannan gaɓa, zan bayyana irin matsalolin da masu dauke da wannan matsalar ke fuskanta a kasar nan.

Da farko dai a yanzu da na ke rubutun nan, akwai mata daruruwa da kusan ma’ajiyar fitsarinsu (Jikkar fitsari) ta riga ta samu matsalar da sai manyan kwararrun likitoci kadai zasu iya masu aikin da zasu warke su koma ga iyalansu. Wasunsu sai an yi masu wani kanikanci sannan a sama masu wata jikkar ajiyar fitsarin gaba daya.
Haka kuma, ba kamar yawancin cututtuka ba inda likitan da bai kware ba zai iya kasancewa shine na farko da zai yi ma mara lafiya aiki, ita matsalar yoyon fitsari matsala ce da ake son kwararren likita ya kasance shine na farko da zai yi ma macen da ta samu sabuwar matsalar yoyon fitsari aiki don ta samu warkewa karon farko na aikin.

Dalilin wannan shine idan a karon farko aka samu matsala wajen yin aikin, to matsalar zata zama mai sarkakiyar da ba kowane likita ne zai iya yi ma mai matsalar aiki ta warke.

Abu na gaba shine kasancewar yawancin masu matsalar marasa karfi ne, likitoci kalilan ne ke zabar zama likitan yoyon fitsari don kwarewa a bangaren ganin ba likitanci ba ne da ke kawo kudi.

Idan muka koma ga asalin dalilin samuwar wannan matsala ga mata, za mu ga cewa daukar lokaci mai tsawo mace na nakuda ke sa matsalar na faruwa.

Dalilin hakan ya sa ta zama matsala ce da ta fi shafar mutane marasa galihu domin su ne dalilai da dama ke hana su zuwa asibiti idan suna da ciki domin awo da kuma lokacin haihuwa idan sun fara nakuda.

Haka nan kuma, wata babbar matsalar da masu fama da wannan matsalar ke fuskanta ita ce yadda ‘yan uwansu ke guje masu musamman mazajen su. Wannan na sa su shiga matsaloli kala kala ciki har da baracebarace da kamuwa da wasu cututtukan da rashin abinci da muhalli mai kyau ke kawowa.

Idan muna maganar mafita kuma idan zamu gaya ma kan mu gaskiya, ya zama dole gwamnatoci a matakai ukkun da muke da su (Tarayya, jihoji da kananan hukumomi) su maida hankali ga samar da hanyoyin hana kamuwa da wannan matsalar da kuma hanyoyin kawar da matsalar.

Zai dace su duba matsalolin asibitocin nan domin magance su. Matsaloli irin na rashin isassun kayan aiki da zai sa a rinka yi ma masu matsalar aiki kyauta cikin gaggawa.

Idan kuma har abin ya yi ma gwamnati yawa, sauran ma’aikatun da ba na gwamnati ba kamar manyan kamfanoni da bankuna da manyan masu kudi suna da rawar da zasu taka domin magancewa da hana wannan matsalar ta yoyon fitsari.

Haka nan kuma shugabannin al’umma, wadanda su ne ke zaune da jama’a, su kara kaimi wajen wayar da kan al’ummar su bisa muhimmancin zuwa asibiti, yin hakan ne kawai zai ba likitoci damar daukar matakin kariya lokacin nakuda.

Haka nan kuma su maida hankali wajen tabbatarwa ƴannuwan wadda ta samu matsalar kada su guje ta a lokacin tana cikin matsalar da bayan ta warke kamar yadda bahaushe ke cewa hannunka ba ya rubewa ka yanke ka ya yar.
A bangaren gwamnati kuma, ya zama dole su maida hankali wajen samar da kayan aiki a asibitoci da kwararrun ma’aikata, zuwa asibiti a tarar da wadanan abubuwa guda biyu (Kayan aiki da kwararrun ma’aikata) ne zai ba jama’a kwarin gwiwar zuwa asibiti duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Karin abinda ake bukata kuma shine samar da motar alɗaukar marassa lafi wadda za ta kasance cikin shiri a duk lokacin da mara lafiya ke neman kulawar da ta fi karfin kananan asibitoci.
Duk wadannan ba wasu abubuwan da ba a iyawa ba ne in dai har akwai niyyar kawo gyaran. Mu tuna cewa ubangiji zai tambayemu yadda mu ka gudanar da amanar da ya bamu.

 

Comments are closed.