Take a fresh look at your lifestyle.

An Samu Bullar Polio A Jihar Sokoto

Hadiza Halliru Muhammad, Sokoto

156

Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa an samu rahotannin bullar cutar Polio a wasu kananan hukumomi biyu a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin  Najeriya da suka hada da Sokoto ta arewa da kuma sokoto ta Kudi.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Dakta Sa’ad Abubakar wanda ya samu wakilcin Wazirin Sakkwato Farfesa Wali Sambo Junaidu yayin gaddamar da yaki da kawar da cutar polio a fadar sarkin musulmi da ke Sakkwato yace majalisar Sarkin Musulmi ta dukufa wajen ganin ta ci gaba da yaki da kawar da duk wata cuta mai kashe yara domin ceto rayuka ya kuma ce za a ci gaba da daukar matakan kawar da cutar shan inna kamar yadda aka kawar a shekarar 2020.

Sarkin ya ce za a iya kawar da cutar shan inna idan yan’kasa suka rungumi tsaftace muhalli, ya Kuma bukaci iyaye da su bada cikakken gowon baya domin yi wa yaransu allurar rigakafi.

Kamar yadda masana kiwon lafiya suka fitar cewa jihar Sakkwato ke kan gaba da adadi 61 bisa ga kididiga yace kiwon lafiya wani muhimmin al’amari ne na rayuwa.

Idan za a tunawa rahotannin baya-bayannan da Asusun tallafawa kana nan yara UNICEF ya fitar na nuna wasu kananan hukumomi 100 na Najeriya basu kammala allurar rigakafi ba, inda jihar Sakkwato ke kan gaba da kananan hukumomi 22 wadanda basuyi allurar rigakafi ba.

A saurari cikon rahoton daga wakiliyar Muryar Najeriya Hadiza Haliru Muhammad daga Sokoto.

Comments are closed.