Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisa Za Ta Kawo Karshen Matsalar Karancin Ruwa A Fika da Ngelzarma

302

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayyar Najeriya da ta gaggauta samar da rijiyoyin burtsatse a garuruwan Fika da Ngelzarma na jihar Yobe a arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan na daga cikin bukatun majalisar a wani kudiri da Honarabul Muhammed Buba Jajere dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Fika/Fune daga jihar Yobe ya gabatar a ranar Alhamis, kan bukatar magance matsalar karancin ruwa a garuruwan Fika da Ngelzarma.

Da yake jagorantar muhawarar, Jajere, ya bayyana cewa garuruwan Fika da Ngelzarma na mazabar tarayya ta FIka/Fune na da yawan jama’a, kuma yawan mutanen wadannan garuruwan na ci gaba da karuwa tsawon shekaru.

Ya ce garuruwan sun dade suna fama da karancin ruwa wanda ke ci gaba da zama babban kalubale ga mazauna yankin wanda hakan ya yi illa ga ci gaba da bunkasar rayuwarsu ta noma da kiwo.

Dan majalisar ya ce samun ruwa mai tsafta na daya daga cikin bukatu na yau da kullum domin dorewar lafiya da walwalar kowane mutum, sannan kuma yana taimakawa wajen gudanar da ayyukan noma don bunkasar tattalin arziki.

Honarabul Mohammed Buba ya bayyana cewa akwai bukatar daukar kwakkwaran matakai tare da hadin gwiwar gwamnatocin kananan hukumomi da jiha da tarayya wajen magance matsalar karancin ruwa a wadannan garuruwan domin rage waharlalun da jama’a ke fuskanta.

Kazalika, yace ana matukar bukatar daukar matakan da suka dace da hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomi da jiha da gwamnatin tarayya domin dakile barkewar annoba a cikin kananan hukumomin.

Da take amincewa da kudirin, majalisar ta bukaci ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da ta gaggauta samar da rijiyoyin burtsatse, da kuma hanyoyin rarraba ruwan a garuruwan Fika da Ngelzarma.

Haka kuma ta umurci kwamitocinta na albarkatun ruwa da hukumar raya arewa maso gabas (NEDC) da su tabbatar da an aiwatar da bukatar yadda ya kamata.

Ak

Comments are closed.