Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Najeriya Ta Nemi Hadin kai Gaggarumi Domin Yaki Da Rashin Tsaro

92

Gwamnatin Najeriya ta yi kira da a dauki matakin bai daya da hadin kai domin yakar matsalar ‘yan fashi da makami da tada kayar baya da kuma rashin tsaro a kasar.

 

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake yin Allah wadai da sace ‘yan gudun hijirar da wasu gungun ‘yan ta’adda na ISWAP suka yi a unguwar Wurge da ke karamar hukumar Ngala a jihar Borno.

 

Ya kuma yi Allah wadai da sace ‘yan makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS) Kuriga da ke gundumar Gwagwada a karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna da wasu ‘yan bindiga suka yi.

 

Idris ya bayyana wannan aika-aika a matsayin mafi girman nau’in rashin mutuntaka wanda bai kamata a amince da shi da wani dalili ba.

 

Yace; “Wadannan sace-sacen ba za su iya karbuwa ba kuma sun sabawa dukkan muhimman dabi’un dan Adam. Gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen yaki da duk wani nau’i na tashin hankali ko tilastawa jama’a da ba su ji ba ba su gani ba, musamman wadanda suka fi kowa rauni a cikinmu. ‘Ya’yanmu sun cancanci neman ilimi a yanayin da babu cutarwa ko barazanar cutarwa, kuma duk wata barazana da za ta kawo musu dauki, harin kai tsaye ne ga makomar kasarmu.”

 

Yayin da yake jajanta wa iyalai da al’ummomin da wannan lamari ya rutsa da su, Ministan ya ce “Shugaban kasa ya umurci hukumomin tsaro da su hanzarta tabbatar da ganin an dawo da duk wadanda aka sace lafiya, tare da kamo wadanda suka aikata laifin. Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin mun yi adalci ga wadanda abin ya shafa da kuma kudurinmu na ganin mun hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki da bin doka da oda.”

 

Idris ya kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu amma su kiyaye tare da bayar da duk wani bayani da zai taimaka wa jami’an tsaro.

 

Ya kuma kara jaddada aniyar gwamnati na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, kuma za ta ci gaba da yin aiki tukuru don ganin cewa karfin masu aikata laifuka na kaddamar da wadannan hare-hare ya kasance a ko da yaushe kuma ba za a iya komawa baya ba.

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.