Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Rasha Ta Ba Wa Koriya Ta Arewa Gangar Mai Miliyoyin

389

An kiyasta cewa Rasha ta baiwa Koriya ta Arewa sama da ganga miliyan daya na mai tun daga watan Maris din wannan shekara, kamar yadda bincike kan hotunan tauraron dan adam daga cibiyar Open Source, wata kungiyar bincike mai zaman kanta da ke da zama a Burtaniya.

 

Ana biyan man fetur a madadin makamai da kuma sojojin Pyongyang ta aikazuwa Masko a yakin da kasar keyi da Ukraine, kamar yadda manyan masana da sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy suka shaida wa BBC.

 

“Wannan ya sabawa takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Masko, wanda ya haramtawa kasashe sayar da man fetur ga Koriya ta Arewa, sai dai kadan, a kokarin da take yi na dakile tattalin arzikinta, don hana ta ci gaba da kera makaman kare dangi”.

 

Hotunan tauraron dan adam, wadanda aka raba su ga BBC, sun nuna fiye da wasu tankokin mai daban-daban na Koriya ta Arewa da suka isa tashar mai a Gabas Mai Nisa na Rasha, sau 43 a cikin watanni takwas da suka gabata.

Wasu Hotunan da aka dauka na jiragen ruwa a teku, sun nuna yadda tankokin suka isa babu kowa, kuma sun kusan cika.

 

Koriya ta Arewa ita ce kasa daya tilo a duniya da aka hana ta siyan mai a kasuwannin bayan fage. Adadin gangar mai tace man da Majalisar Dinkin Duniya za ta iya karba a kowace shekara ya kai 500,000, wanda ya yi kasa da adadin da take bukata.

 

“Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ba ta amsa bukatar mu ta yin sharhi ba”.

 

Canja wurin mai na farko da Cibiyar Open Source ta rubuta a cikin wani sabon rahoto, ya kasance a ranar 7 ga Maris 2024, watanni bakwai bayan da aka fara bayyana Pyongyang na aika makamai zuwa Masko.

 

An ci gaba da jigilar kayayyaki yayin da aka ce an aike da dubunnan sojojin Koriya ta Arewa zuwa Rasha don fafatawa, inda aka samu wadanda aka tura na karshe a ranar 5 ga watan Nuwamba.

 

“Yayin da Kim Jong Un ke bai wa Vladimir Putin hanyar rayuwa donmi ci gaba da yakin shi, Rasha ta yi shiru tana baiwa Koriya ta Arewa hanyar rayuwa ta kanta,” in ji Joe Byrne daga Cibiyar Open Source.

 

“Wannan ci gaba da kwararar mai ya baiwa Koriya ta Arewa matakin kwanciyar hankali da ba ta samu ba tun lokacin da aka shigar da wadannan takunkumi.”

 

Tsofaffin mambobin kwamitin Majalisar Dinkin Duniya hudu da ke da alhakin bin diddigin takunkumin da aka kakabawa Koriya ta Arewa, sun shaida wa BBC cewa an mika su ne sakamakon kara alaka tsakanin Masko da Pyongyang.

 

Hugh Griffiths, wanda ya jagoranci kwamitin daga 2014 zuwa 2019 ya ce “Wadannan canja wurin suna kara rura wutar inji Putin – wannan man ne don makamai masu linzami, da kuma manyan bindigogi kuma yanzu mai ga sojoji.”

 

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya shaida wa BBC cikin wata sanarwa cewa: “Don ci gaba da yaki a Ukraine, Rasha ta kara dogaro ga Koriya ta Arewa wajen samun sojoji da makamai domin musanya da mai.”

 

Ya kara da cewa hakan yana “yin tasiri kai tsaye kan tsaro a yankin Koriya, Turai da Indo-Pacific”.

 

 

BBC/Ladan Nasidi.

Comments are closed.