Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Koma Abuja Bayan Ziyarar Bikin Rantsarwa A Ghana

3,137

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya koma Abuja babban birnin kasar bayan halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar Ghana na 32 John Dramani Mahama.

 

Jirgin shugaban ya sauka ne da yammacin ranar Talata a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da karfe 9:30 na dare inda mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila da sauran manyan jami’an tsaro suka tarbe shi.

 

Shugaba Tinubu a birnin Accra a matsayin babban bako na musamman a bikin rantsar da shugaba Dramani Mahama ya yaba da mulkin dimokuradiyya a Afirka ya ce nasarar mika mulki ga dimokaradiyya a Ghana da sauran kasashen Afirka ya dora tambayoyi kan irin karfin dimokuradiyya da kuma kokarin da nahiyar ke da shi.

 

Shugaban na Najeriya ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.

 

Ya kuma yi kira da a samar da tsarin bai daya domin tinkarar matsalolin talauci da rashin aikin yi ga matasa da rashin zaman lafiya da tada kayar bay da sauran kalubalen dake kawo cikas ga ci gaban yankin.

 

Idan dai za a iya tunawa shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa Legas ranar 18 ga watan Disamba inda ya yi bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

 

Shugaban kasar a lokacin da ya ke Legas ya gana da shugabannin majalisar dokokin kasar da tsoffin manyan hafsoshin majalisar karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

A wajen taron, shugaba Tinubu ya jaddada aniyar sa na jagorantar Najeriya zuwa makoma mai albarka.

 

Ya jaddada cewa jin dadin ‘yan Najeriya shine jigon kokarin gwamnatin sa.

 

Shugaban na Najeriya a gidan shi da ke Legas ya kuma karbi bakuncin ‘yan kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) inda ya bukaci gwamnonin da su ba da fifiko ga ci gaban kananan hukumomi.

 

A wajen taron Gwamnonin jihohin kasar 36 sun jaddada aniyarsu ta yin aiki karkashin jagorancin shugaba Tinubu da hada kai da gwamnatinsa wajen ciyar da kasa gaba.

 

Shugaba Tinubu ya kuma karbi bakuncin Mai Martaba Sarki Awujale na Ijebuland Oba Sikiru Kayode Adetona Ogbagba II.

Shugaban a gidan shi na ikoyi tare da Awujale ya jaddada kudirin gwamnatin shi na karfafa hadin gwiwa da shugabannin gargajiya.

 

Ya yaba da gagarumin rawar da cibiyoyin gargajiya ke takawa wajen samar da hadin kan kasa da bunkasar tattalin arziki da shugabanci a matakai daban-daban.

 

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.