Take a fresh look at your lifestyle.

Garkuwa da Mutane Na Gab Da Zama Tarihi a Najeriya: Ribado

Shehu Salman, Sokoto.

89

Ayyukan ta’addanci da suka haɗa da sata da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da su ka dagula al’amurra musamman a yankin arewa maso yammacin Najeriya na kan hanyarsu ta zama tarihi duba da yadda gwamnati karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ya jajirce wajen yaƙi da masu tada zaune tsaye a ko ina suke a faɗin ƙasar.

Ayyukan dai na ƴan ta’adda sun durkusar da noma da fatauci a wadannan yankunan da ma duk inda ake fama da makamantan wadannan rigingimu da ya haɗa da yankin kudu maso gabacin ƙasar nan a cewar mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo yayin wata ƙasida da ya gabatar a wajentaron yaye ɗalibai karo na 38,39,40 da kuma 41 da jami’ar Usmanu Danfodiyo ta gudanar.

“Tun shigowar wannan gwamnatin yan watannin da suka shuɗe an samu nasarar daƙile ayyukan Yan a ware na IPOB a yankin kudu maso gabaci, haka ma masu garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammaci babu wani ɗalibi ƙwaya guda da ke hannun wadannan ɓata gari, kaf an karɓosu da ƙarfin tuwo ba tare da biyan ko ƙwabo ba da sunan kuɗin fansa. ” In ji Ribado

Haka zalika, Mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro ya tabbatar da ƙudurorinsu a gwamnatance na sake gina sabuwar Najeriya wadda ta ke cike da aminci kuma za ta kula rayuwar al’ummar da ta ke jagoranci, gwamnatin shugaban Tinubu a cewar Malam Nuhu Ribaɗo mai sauraren koke-koken al’umma ce domin kuwa al’ummar sune a gabansu.

“Da sannu manoma da yan kasuwa za su koma harkokinsu ba tare da shayin komai ba da zarar aminci ya dawo kamar yadda ya ke a baya.”

Da kuma ya ke tsokaci kan tattalin arzikin ƙasar, Malam Nuhu Ribaɗo ya ce shugaba Tinubu ya yi amfani da gogewarsa wajen bijirowa da wasu sabbin dabaru da suka ƙara darajar kuɗin ƙasar bisa kuɗin dalar Amurka da ta zame wa ƙasar ƙarfen ƙafa.

Shirin dai na shugaba Tinubu na samar da sabuwar Najeriya da za ta shawo kan matsalolin tsaro da kuma inganta tattalin arzikin kasa da na al’umma.

Abdulkarim

Comments are closed.