Isra’ila ta ba da umarnin dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci na Isra’ila zuwa Paphos a Cyprus saboda wasu dalilai na tsaro da ba a bayyana ba kamar yadda jami’ai suka tabbatar.
Rahotanni daga Isra’ila na cewa, hukumar tsaron cikin gida Shin Bet ta ba da umarnin dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa tashar jirgin, tashar da aka fi daukar nauyin zirga-zirgar ababen hawa a yammacin gabar tekun Cyprus.
“Jamhuriyar Cyprus tana sane da canjin jadawalin saboda dalilai na tsaro, na kamfanonin Isra’ila daga da kuma zuwa tashar jirgin saman Paphos. Hakan ya faru ne kwanaki kadan da suka gabata,” in ji wani jami’in Cyprus.
Jami’in ya kara da cewa jiragen saman Isra’ila na ci gaba da zuwa Larnaca bisa ka’ida yayin da yake magana kan babban filin jirgin saman kasa da kasa na Cyprus.
Paphos shine mafi ƙanƙanta na filayen jirgin saman Cyprus biyu kuma yana da wani sansanin soja da Amurka ta tsara don haɓakawa.
Dangane da jadawalin jirgin lokacin hunturu da ake samu akan layi, ana samun jirage har 10 a mako daga Tel Aviv da jirage 7 a mako daga Haifa.
Ladan Nasidi