‘Yan tawayen M23 na Kongo sun shiga tsakiyar birnin Goma da ke gabashin kasar a ranar Litinin kamar yadda shaidu biyu suka bayyana sa’o’i kadan bayan da suka yi ikirarin kwace birnin duk da cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a kawo karshen farmakin.
Ba a dai fayyace ko kawancen ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda sun kwace daukacin birnin da ke gefen tafkin ba. A filin tashi da saukar jiragen an rage wasu daga cikin sojojin da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda mazauna yankin, da wani jami’in yankin da majiyar Majalisar Dinkin Duniya ta ce.
Mayakan da ke samun goyon bayan Rwanda a ranar Lahadi sun rufe birnin Goma mafi girma a gabashin Kongo lamarin da ya tilastawa dubban fararen hula tserewa tare da dakatar da tashin jiragen sama daga filin jirgin saman yankin yayin da dakarun gwamnati ke fafatawa don hana ‘yan tawayen kwace birnin.
Ci gaban ‘yan tawayen na baya-bayan nan ya tilastawa dubban mutane a gabashin Kongo masu arzikin ma’adinai barin gidajensu tare da haifar da fargabar cewa rikicin da aka shafe shekaru da dama ana yi yana fuskantar hadarin sake barkewar yakin yanki.
“Akwai rudani a cikin garin; a nan kusa da filin jirgin, mun ga sojoji. Har yanzu ban ga M23 ba” inji wani mazaunin garin. “Akwai kuma wasu lokuta na sace-sacen shaguna.” Inji Rahotanni.
Mazauna yankin sun ce ana iya jin karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin sama, da tsakiyar birnin da kuma kusa da kan iyaka da Rwanda.
Tryphon Kin-Kiey Mulumba, shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama, ya ce sojojin na ci gaba da kula da filin jirgin.
Bidiyon da ba a tantance ba da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna mazauna yankin suna kwasar kaya a wajen dakin ajiyar kwastam na filin jirgin da ginshikan mutane dauke da muggan makamai, wadanda ake kyautata zaton mayakan M23 ne.
Har yanzu dai ba a iya tantance ko wanene ke da alhakin harbin ba, amma wani mazaunin garin ya ce akwai yiwuwar harbin gargadi ne ba fada ba.
‘Yan tawayen sun umurci sojojin gwamnati da su mika wuya da karfe 0300 a ranar Litinin (0100 GMT) kuma sojojin Congo 100 sun mika makamansu ga sojojin Uruguay a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Congo (MONUSCO) in ji rundunar sojin Uruguay.
Ma’aikatan MONUSCO da iyalansu suna ta kaura daga kan iyaka zuwa kasar Rwanda a safiyar ranar Litinin inda motocin bas 10 ke jiran daukar su.
Ladan Nasidi.