Take a fresh look at your lifestyle.

Firaministan Chadi Ya Gabatar Da Bukatar Soke Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

32

Tsohon abokin hamayyar  Firayim Ministan Chadi  wanda ya yi yunkurin shiga mulkin soja kuma ya yi takara da shugaban rikon kwarya, Succes Masra, ya yi jawabi ga manema labarai a gidan shi da ke N’Djamena a ranar 8 ga Mayu, 2024, kwanaki biyu bayan zaben shugaban kasar.

 

Firaministan kasar Chadi na rikon kwarya Sucés Masra ya shigar da kara a majalisar dokokin kasar yana kalubalantar sakamakon farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon jiya.

 

An ayyana ubangidansa Janar Mahamat Deby ne a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 61% na kuri’un da aka kada, amma Mista Masra na daukar kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.

 

“Tare da taimakon lauyoyinmu, a yau mun mika bukatar ga Majalisar Tsarin Mulki ta bayyana gaskiyar akwatunan zabe,” in ji Mista Masra a wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta ranar Lahadi.

 

 

 

Dan adawar da jam’iyyarsa ta Transformers sun ce ya kamata a soke sakamakon zaben, inda suka yi zargin cewa an cika wasu akwatunan zabe, wasu kuma sojoji suka tafi da su domin a kirga su a wani waje.

 

Jam’iyyar ta kara da cewa an kama wasu ‘yan adawa, yayin da aka yi wa Mista Masra da magoya bayan shi barazana.

 

Duk da haka, Mista Masra ya sake nanata cewa mabiyansa sun kasance “masu zaman lafiya saboda kaunar kasarmu”, yana mai dagewa cewa “canjin da kuke son gani ba zai iya faruwa a cikin kasa mai lalacewa ba”.

 

Jim kadan gabanin bayyana sakamakon zaben, Mista Masra ya bukaci magoya bayansa da su tashi tsaye tare da gudanar da zanga-zangar lumana domin kare kuri’unsu.

 

A cikin kwanaki masu zuwa ne majalisar tsarin mulkin kasar za ta yanke shawara kan ko za ta amince da sakamakon farko na zaben ko kuma ta soke shi, kamar yadda Mista Masra da Yacine Abdramane Sakine, wani dan takara da ya sha kaye a zaben suka bukata.

 

Ko da yake har yanzu majalisar ba ta tabbatar da Mista Déby a matsayin sabon shugaban kasar Chadi ba, tuni wasu shugabannin kasashe irin su Bola Tinubu na Najeriya da Umaro Sissoco Embalo na Guinea Bissau suka taya shugaban sojin kasar murna.

 

 

BBC/Ladan Nasidi.

Comments are closed.