Babban Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), Mista Kashifu Inuwa, ya yi kira da a sauya sheka daga sana’ar gargajiya zuwa tsarin tattalin arziki na zamani wanda zai haifar da kirkire-kirkire a fadin Arewacin Najeriya.
Mista Inuwa ya yi wannan kiran ne a taron Future Map Foundation Roundtable 1.0 (North-West Edition) da aka gudanar a Kano, inda ya jaddada cewa tafiyar hawainiyar da yankin ke samu ba don rashin hazaka ba ne, sai dai rashin tsarin hadin kai da niyya.
Ya jaddada bukatar kara karfafa hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin ilimi, kungiyoyi masu zaman kansu, ‘yan kasuwa, da gwamnati, yana mai cewa duk da cewa dole ne gwamnati ta samar da tsare-tsare da yanayin da ya dace, kamfanoni masu zaman kansu sun kasance babban tushen kirkire-kirkire.
A cewarsa, dole ne kirkire-kirkire su kasance masu dogaro da jama’a kuma su kasance cikin gida don cimma gasa a duniya, yana mai kira ga yankin da ya tashi daga amfani da fasahar zamani zuwa samar da hanyoyin da suka dace da kalubalen cikin gida.
Zauren ya tattaro masu tsara manufofi, masu samar da fasaha, da shugabannin muhalli don hada kai don samar da taswirar ci gaba mai dorewa don sauyin dijital na Arewa maso Yamma.
Mahalarta taron sun yi alkawarin karfafa manufofin kirkire-kirkire na yanki da zurfafa hadin gwiwar jama’a da masu zaman kansu don kara habaka ci gaban dijital a yankin.
Shirin ya yi dai-dai da ajandar sabunta bege na Gwamnatin Tarayya, wanda ke da nufin cimma kashi 95 cikin 100 na ilimin zamani a duk fadin kasar nan da shekara ta 2030
Aisha. Yahaya, Lagos