Wani jirgin ruwan dakon kaya na kasar Norway tare da ma’aikatan Rasha duka da ake zargi da lalata layin wayar tarho na tekun Baltic hukumomi a Norway sun saki wani jirgin ruwan dakon kaya bayan da ba a sami wata alaka da lamarin ba in ji ‘yan sanda.
An kama Silver Dania ne bisa bukatar hukumomin Latvia da taimakon jami’an tsaron gabar tekun Norway kamar yadda ‘yan sanda a birnin Tromsoe da ke arewacin Norway suka ce a baya.
“Za a ci gaba da binciken, amma ba mu ga dalilin da zai sa jirgin ya ci gaba da zama a Tromsoe ba. Babu wani bincike da aka samu da ke alakanta jirgin da aikin lalata igiyar ruwa a karkashin teku,” in ji ‘yan sandan a cikin wata sanarwa.
Mai kamfanin Silver Dania kungiyar jigilar kayayyaki ta tekun Silver ta musanta cewa jirgin na da hannu a lamarin kamar yadda kafar yada labarai ta Norway ta ruwaito.
Kasashen Sweden da Latvia na gudanar da bincike kan zargin yin zagon kasa da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata na kebul din da ya hada kasashen biyu.
‘Yan sandan Sweden sun kama tare da shiga jirgin ruwan dakon kaya Vezhen dake dauke da tutar Malta bisa zarginsa da yin barna.
Shugaban kamfanin Vezhen’s wani kamfani na Bulgaria ya ce a ranar Litinin mai yiwuwa ya bugi kebul din da anginsa amma ya musanta wata mugun nufi.
Mats Ljungqvist mai gabatar da kara da ke gudanar da bincike a Sweden ya ce sun duba jirgin Norway amma ya yi watsi da batun.
Yankin Tekun Baltic na cikin shirin ko-ta-kwana bayan an katse wutar lantarki hanyoyin sadarwa da bututun iskar gas tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a shekarar 2022.
Kwanan nan kawancen sojan NATO ya karfafa kasancewarsa da jiragen ruwa, jiragen sama da jiragen yaki marasa matuka.
REUTERS/ Ladan Nasidi.