Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro A Pakistan

100

Sojoji 18 da ‘yan ta’adda 24 ne aka kashe a fadan da aka gwabza a kudu maso yammacin Pakistan in ji bangaren yada labaran soja.

 

‘Yan ta’addan sun yi kokarin kafa shingayen ne da daddare a lardin Balochistan mai fama da rikici kuma akasarin mace-macen sun faru ne yayin da jami’an tsaro suka kwashe su in ji rundunar.

 

An kashe 11 daga cikin ‘yan ta’addan a wani abin da sojoji suka bayyana a matsayin “ayyukan share fage” a ranar Asabar.

 

Kawo yanzu dai ba a bayyana ko wace kungiya ce ‘yan bindigar ba.

 

A halin da ake ciki Firayim Ministan Pakistan, Shehbaz Sharif a cikin wata sanarwa ya yi Allah wadai da harin.

 

Lardi mai arzikin ma’adinai mai iyaka da Iran da Afganistan ya sha fama da tashe tashen hankula na tsawon shekaru 10 daga kungiyoyin ‘yan aware na Baloch da masu kishin Islama su ma suna kai farmaki a can.

 

A ranar Talata a wani lamari na daban an tarwatsa masu tsattsauran ra’ayin Islama a cikin wata mota dauke da bama-bamai a yunkurinsu na kutsawa ofishin jami’an tsaron Pakistan da ke kusa da kan iyaka da Afghanistan.

 

A cikin watan Agusta, akalla mutane 73 ne suka mutu a Balochistan, lokacin da mayakan ‘yan aware suka kai hari a ofisoshin ‘yan sanda, da layin dogo, da manyan tituna, inda jami’an tsaro suka kaddamar da harin ramuwar gayya.

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.