Take a fresh look at your lifestyle.

Turkiyya Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 23 A Sham

280

Turkiyya ta ce ta kashe mayakan Kurdawa 23 a arewacin Siriya wanda shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren da ta kai musu tun bayan hawan shugaban Amurka Donald Trump kan karagar mulki a watan jiya.

 

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce mayakan ‘yan ta’addar na kungiyar Kurdawa ta Siriya YPG ne da kuma haramtacciyar jam’iyyar Kurdistan Workers Party ko PKK.

 

Turkiyya na kallon PKK da YPG a matsayin kungiyoyi daban-daban inda Amurka ke kallonsu a matsayin kungiyoyi daban-daban bayan da ta haramta PKK a matsayin ‘yan ta’adda amma ta dauki YPG a matsayin manyan kawayenta a Siriya a yakin da ake yi da IS.

 

Turkiyya ta dade tana yin kira ga Washington da ta janye goyon bayan da take baiwa kungiyar YPG tare da bayyana fatan Trump zai yi gyara ga manufofin gwamnatin da ta gabata ta shugaba Joe Biden.

 

Dakarun Turkiyya da kawayensu a Siriya sun sha fafatawa da mayakan Kurdawa a can tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar Al-Assad na Siriya a watan Disamba.

 

Turkiya ta ce dakarun Syrian Democratic Forces, ko SDF wata kungiya mai goyon bayan Amurka da ta hada da Kurdawa YPG – dole ne su kwance damara ko kuma su fuskanci shiga tsakani na soji.

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.