Take a fresh look at your lifestyle.

Koriya Ta Arewa Ta Yi Allah-wadai Da Shawarar Da Trump Ya Yi Na Mamaye Gaza

118

Koriya ta Arewa ta yi Allah-wadai da shawarar shugaban Amurka Donald Trump na mamaye Gaza da kuma mayar da Falasdinawa matsuguni a matsayin abin kunya tare da zargin Washington da yin fashi.

 

Shawarar ta ruguje da danyen fata da Falasdinawa ke da shi na samar da tsaro da zaman lafiya kamar yadda wani sharhin da kamfanin dillancin labaran Koriya ta tsakiya (KCNA) ya bayar ba tare da bayyana sunan Trump kai tsaye ba.

 

KCNA ta ce “Duniya yanzu tana tafasa kamar tukunyar porridge a kan sanarwar fashewar bam na Amurka,” in ji KCNA.

 

Sharhin na nufin sanarwar girgizar da Trump ya yi cewa Amurka na da niyyar kawar da mazauna Gaza tare da mayar da yankin da yaki ya daidaita zuwa abin da shugaban ya kira a matsayin “Riviera na Gabas ta Tsakiya”.

 

Sharhin na KCNA ya kuma soki gwamnatin Trump kan kiran da ta yi na karbe mashigin ruwan Panama da Greenland da kuma shawarar da ta yi na sauya sunan “Gulf of Mexico” zuwa “Gulf of America”.

 

Rahoton na KCNA ya ce “Ya kamata Amurka ta farka daga mafarkin da ta yi na yau da kullun, sannan ta dakatar da aiwatar da keta mutunci da ‘yancin sauran kasashe da al’ummomi,” in ji rahoton na KCNA yayin da ya kira Amurka a matsayin “muguwar dan fashi.”

 

Trump ya yi wani taron koli da ba a taba ganin irinsa ba da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a wa’adin mulkinsa na farko kuma ya bayyana irin dangantakar da ke tsakaninsu.

 

Kwanan nan shugaban na Amurka ya ce zai sake ganawa da Kim, ko da yake ya zuwa yanzu da kyar kafafen yada labaran gwamnatin Pyongyang suka yi tsokaci kan wa’adin Trump na biyu yayin da suke ci gaba da yin tofin Allah tsine kan abin da suke kallo a matsayin babbar barazanar tsaro da Washington da kawayenta ke yi.

 

Koriya ta Arewa wacce sau da yawa ke jayayya kan ra’ayoyin kasashen yamma kan batutuwan kasa da kasa ta yi kakkausar suka kan halin da ake ciki a Gaza inda ta dora alhakin zubar da jinin Isra’ila tare da kiran Amurka a matsayin “mai hannun jari.”

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.