A ranar Alhamis ne aka mayar da dakarun kiyaye zaman lafiya 14 na kasar Afirka ta Kudu SANDF wadanda suka rasa rayukansu a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo zuwa kasar Afirka ta Kudu. An karrama sojojin ne da wani biki a sansanin sojin sama da ke Pretoria.
Shugaba Cyril Ramaphosa wanda ke jawabi a bikin ya jinjinawa bajinta da sadaukarwar sojojin. Ya ce, “An kira su ne da su yi aikin wanzar da zaman lafiya a duk fadin nahiyarmu da ma na kasa da kasa kuma sun amsa wannan kira da karfin hali. A matsayinmu na al’umma muna alfahari da jajirtattun sojojinmu. Mun girmama aikinmu ta hanyar dawo da su gida.”
An kashe sojojin ne a watan da ya gabata a wani kazamin fada tsakanin sojojin DRC da ‘yan tawayen M23. Mummunan lamarin ya yi nuni da irin mawuyacin halin da dakarun wanzar da zaman lafiya ke fuskanta yayin da suke kokarin daidaita yankunan da rikici ya shafa.
Shugaba Ramaphosa ya kara jaddada muhimmancin aikin sojojin a DRC. “Kuma mu a matsayinmu na ‘yan Afirka ta Kudu muna daukar su a matsayin jaruman al’ummarmu. Ayyukansu a DRC ba wai kawai kiyaye tsari ba ne. Ya shafi gina gadoji samar da zaman lafiya, samar da fahimta, da samar da hanyoyin samar da dawwamammen zaman lafiya a yankinmu da nahiyarmu,” inji shi.
Jami’an sojojin saman kasar ne dauke da akwatunan gawar sojojin da aka lullube da tutocin kasar Afirka ta Kudu. Daga nan ne aka mika gawarwakin ga iyalansu da ke cikin makoki wadanda suka halarci bikin karrama ‘yan uwansu.
Wannan biki mai ratsa jiki ya zama abin tunatarwa kan sadaukarwar da wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya suka yi da kuma jajircewar da Afirka ta Kudu ta yi na ba da gudummawa ga kokarin samar da zaman lafiya a fadin Afirka da ma duniya baki daya.
Africanews/Ladan Nasidi.