Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Majalisa Sun Koka Don Hana Wani Yajin Aikin Kungiyar Kwadago

497

Majalisar Wakilai ta kuduri aniyar tattaunawa da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, kan barazanar da ta ke yi na daukar wani mataki a masana’antu kan sabon mafi karancin albashi.

 

Kudurin majalisar ya biyo bayan wani bayani ne da dan majalisa mai wakiltar mazabar Etche/Omuma na jihar Rivers, Mista Kelechi Nwogu ya gabatar.

 

Mataimakin kakakin majalisar, Mista Benjamin Kalu, ya ce shugabannin majalisar za su gana da shugabannin kungiyoyin kwadago kan batun mafi karancin albashi sannan su mika rahotonsu ga majalisar nan da mako guda.

 

Mista Nwogu ya sanar da majalisar cewa kungiyoyin kwadago sun sanar da shirin shiga yajin aikin daga ranar 31 ga watan Mayu, kan takaddamar da ke tsakanin su da gwamnatin tarayya dangane da amincewa da sabon mafi karancin albashi.

 

Dan majalisar wanda ya bayyana cewa akwai bukatar majalisar ta dauki kwararan matakai domin dakile yajin aikin, ya kuma tunatar da cewa a ranar 16 ga watan Maris ne majalisar ta amince da bukatar karin mafi karancin albashi.

 

Ya kuma yi nuni da cewa har yanzu kwamitin da abin ya shafa bai kai rahoto ga majalisar ba, sabanin tanadin dokar zaman majalisar da ta umarci kwamitoci su kammala ayyukansu cikin kwanaki 30, ana sa ran za a kara wa’adin.

 

“Idan ka lura da doka ta 18 mai lamba 1 Sub 5 na kundin tsarin mulkinmu, ta ce duk wani lamari da aka mika wa wani kwamiti za a yi maganinsa cikin kwanaki 30, in ba haka ba kwamitin zai tsaya bayan kwanaki 60, sai dai an kara wa’adin. Majalisar ta amince da kudirin samar da albashin ma’aikata a Najeriya, wanda mataimakin shugaban marasa rinjaye da sauran su suka dauki nauyi a ranar 16 ga watan Maris. Ya kamata a gabatar da rahoton ga majalisar kafin wannan lokacin,” inji shi.

 

Shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, a cikin gudunmawar da ya bayar, ya lura cewa dole ne majalisar ta dauki matakin gaggawa, “maimakon barin aiki a tafi yajin aiki.”

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.