Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Yi Makokin Yarima Doyin Okupe

1,578

kasar a cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa, Mista Bayo Onanuga ya fitar ya bayyana yadda Yarima Okupe ke dawwama a jiharsa ta haihuwa da kuma irin zurfin rashin da ya bari a cikin zukatan wadanda suka yi mu’amala da shi kai tsaye.

 

Shugaba Tinubu ya Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga ‘yan uwa da abokan arziki da abokan huldar Yarima Doyin Okupe da  likita da dan siyasa mai sadarwa da dabaru wanda ya taka rawar gani a fagen siyasar Najeriya.

 

Shugaban tuno da Dakta Okupe a matsayin jajirtacce kuma mai fafutukar ganin an samar da ci gaban kasa yana mai nuna alhininsa kan rasuwarsa a daidai lokacin da kwarewarsa da basirarsa ke da amfani ga al’umma.

 

Shugaban ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Ogun musamman al’ummar Iperu-Remo wadanda suka yi rashin babban dansa kuma shugaba.

 

“Wani fitaccen dan Iperu-Remo a jihar Ogun, Prince Okupe ya taba zama babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Goodluck Jonathan kan harkokin jama’a da kuma mataimakin shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan harkokin yada labarai.

 

“Yarima Okupe ya bayar da gudunmawa sosai a fannin likitanci a matsayinsa na wanda ya kafa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Royal Cross Legas da mawallafin Life Mirror jarida mai mayar da hankali kan kiwon lafiya.

 

“A lokacin da ya shafe sama da shekaru 30 yana siyasa Okupe ya yi aiki a matsayin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar National Republican Convention (NRC). Ya yi fice a jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Accord Party wadda shi ne shugabanta na kasa.

 

Kwanan nan ya kasance Darakta-Janar na Yakin Neman Shugabancin Jam’iyyar Labour Party na Zaben 2023.

 

Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin da kuma ta’aziyya ga kowa

 

An haifi Adedoyin Ajibike Okupe a ranar 22 ga Maris 1952 wanda aka fi sani da Doyin Okupe likita ne kuma dan siyasa dan Najeriya wanda ya kafa cibiyar kula da lafiya ta Royal Cross kuma ya kasance Sakataren Yada Labarai na National Republican Convention (NRC).

 

Cif Okupe ya kasance dan takarar gwamna a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Ogun.

 

Okupe ya kasance mai yada labarai a lokuta daban-daban ga masu neman takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP ciki har da shugaban kasa Olusegun Obasanjo da shugaban kasa Goodluck Jonathan da Bukola Saraki da mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

 

Cif Doyin Okupe ya shiga jam’iyyar Labour ne gabanin babban zaben Najeriya na 2023 kuma ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar Labour har sai da aka zabi dan takara.

 

 

 

L;ADAN NASIDI.

Comments are closed.