Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Burkina Faso Zai Karbi Kyauta A PALESH 2025

72

Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore na shirin karbar babbar lambar yabo a bugu na 14 na PAN AFRICAN LEADERSHIP SYMPOSIUM AWARDS (PALESH NIGERIA 2025). Wannan karramawar wata shaida ce ga nagartaccen shugabancinsa da kwazonsa wajen gina kasa da ci gaban kawo sauyi a Burkina Faso.

 

Kyautar wacce Majalisar Koli ta UNIPGC ta Afirka ta amince da shi karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar Laberiya, Dokta Jewel Howard Taylor da shugaban UNIPGC na duniya Amb Dr. Jonathan Ojadah ya amince da sadaukarwar Traore ga zaman lafiya da adalci da cibiyoyi masu karfi a matsayin Babban Kwamandan Zaman Lafiya (GCOP).

 

Tun hawansa karagar mulki Shugaba Traore ya aiwatar da kyawawan tsare-tsare don inganta harkokin kiwon lafiya da bunkasa ayyukan noma da bunkasa tattalin arziki. Salon shugabancinsa da shawararsa sun dora kasar Burkina Faso kan turbar ci gaba cikin sauri da samun ‘yancin cin gashin kai lamarin da ya sa aka amince da shi a matsayin jagora a Afirka.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.