An kama wata alkalin babbar kotu a Uganda da jami’ar shari’a ta Majalisar Dinkin Duniya, Lydia Mugambe a karkashin dokar bautar zamani a Burtaniya.
An same ta da laifin safarar mutane da hada baki don tsoratar da wanda aka azabtar a lamarin da ya girgiza masu lura da al’amura.
Hotunan ‘yan sandan sun nuna yadda ta ke nuna rashin imani yayin da jami’an suka sanar da ita tuhumar da ake mata. Ta dage cewa tana da kariyar diflomasiyya kuma ta musanta aikata wani laifi.
A yayin shari’a masu gabatar da kara sun yi zargin cewa Mugambe ya ci zarafin wata budurwa ‘yar Uganda inda ya yaudare ta game da makasudin tafiyar ta zuwa Birtaniya tare da sanya mata rashin adalcin yanayin aiki.
Mai gabatar da kara ta kuma yi ikirarin cewa ta hada baki da mataimakin babban kwamishinan Uganda John Leonard Mugerwa domin saukaka shigar matar cikin kasar. A maimakon haka an yi zargin cewa ta amince ta shiga tsakani a kan batun shari’a da ya shafi Mugerwa.
Wacce aka kash wacce aka kare asalinta ta shaida wa kotun cewa ta ji an ware kuma ta makale a lokacin da take Burtaniya. Mugambe wanda ke neman digirin digirgir a fannin shari’a. a Jami’ar Oxford ta musanta cewa ta tilasta wa matar ta yi aikin da ba a biya ta albashi ba inda ta ce a ko da yaushe tana kyautata mata.
Bayan hukuncin da aka yanke mata ‘yan sandan Thames Valley sun tabbatar da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da duk wata kariya ta diflomasiya da Mugambe ya samu a matsayin alkalin Majalisar.
An ji karar hayaniya a harabar kotun a lokacin da aka yanke hukuncin, kuma an dakatad da shari’ar na dan lokaci bayan da Mugambe ya bayyana rashin lafiya.
Wannan shari’ar ta nuna damuwa da ake ci gaba da yi game da cin gajiyar aiki da kuma yin amfani da gata na diflomasiyya.
Africanews/Ladan Nasidi.