Take a fresh look at your lifestyle.

Jiragen Yaki Na Soja Sun Yi karo Da Wani Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu A Koriya Ta Kudu

70

Wani jirgin yakin Koriya ta Kudu maras matuki ya yi karo da wani jirgin sama mai saukar ungulu a filin jirgin sama lamarin da ya haddasa gobara da aka kashe cikin kimanin mintuna 20 ba tare da an samu asarar rai ba in ji ma’aikatar tsaron Koriya ta Kudu.

 

Rahoton ya ce jirgin Heron Heron ne da Isra’ila ta kera wani babban jirgin leken asiri ne marar matuki kamar yadda rahoton ya bayyana cewa sojoji.

 

Rahoton ya ce babu wani yunkuri da Koriya ta Arewa ta yi na kulle siginar GPS a lokacin da hatsarin ya afku a Yangju da ke arewacin birnin Seoul.

 

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata da irin wannan nau’in jirgin mara matuki ya yi hatsari a yankin guda in ji Yonhap.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.