Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Ya Gana Da Kantoman Jihar Ribas

6,541

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da kantoman jihar Ribas Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a fadar gwamnati dake Abuja.

 

Vice Admiral Ibas wanda tsohon babban hafsan sojin ruwa ne ya isa fadar gwamnatin kasar da karfe 12:50 na rana domin taron, wanda ke zuwa sa’o’i kadan bayan da shugaban kasar ya kafa matakan gaggawa a jihar mai arzikin man fetur.

 

KU KARANTA KUMA: Shugaban Najeriya ya ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers

 

Shugaban ya nada Ibas ne a yammacin ranar Talata da ta gabata don tafiyar da al’amuran jihar Ribas bayan kafa dokar ta-baci a jihar biyo bayan barkewar rikicin siyasa a can.

 

A cikin matakan ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara Mataimakin Gwamna Ngozi Odu da dukkan zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

 

A madadinsu shugaban na Najeriya ya nada Vice Admiral Ibas a matsayin mai gudanar da mulki shi kadai, tare da sanya ido kan harkokin mulki amma ba kafa sabbin dokoki ba.

 

Ya kuma jaddada cewa bangaren shari’a zai ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da kashin kansa ba.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.