Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Kantoman jihar Ribas Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai Ritaya) a fadar gwamnati da ke Abuja babban birnin Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Shugaban Najeriya ya gana da kantoman Ribas
A ranar Laraba ne aka rantsar da Ibas bayan wata ‘yar gajeriyar ganawa da shugaban kasar bayan nadin nasa.
Bikin wanda ya gudana a ofishin shugaban kasa ya samu halartan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a Lateef Fagbemi Babban Sakataren Shugaban Kasa Hakeem Muri-Okunola da kuma mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru Bayo Onanuga.
Shugaban ya yi rantsuwar ne cikin wasu mintuna kafin karfe 3 na rana
Idan dai za a iya tunawa a yammacin ranar Talata ne shugaba Tinubu ya nada Ibas domin tafiyar da al’amuran jihar Ribas bayan da ya kafa dokar ta-baci a jihar biyo bayan rikicin siyasa da ya barke a jihar.
Ladan Nasidi.