Uwargidan shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta taya mijinta murnar cika shekaru 73 da haihuwa.
A cikin sakon da ta fitar a Abuja Uwargidan shugaban kasar ta musamman ta gane kyawawan halaye da suka sa shugaban Najeriyar a wurinta.
Ta kuma yi addu’ar Allah ya ba mijinta lafiya da wadata.
“Ina farin ciki da godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa amincinshi a cikin rayuwarku tsawon shekaru. Ina murna da jajircewarku karfinku da juriyarku wadanda duk suka ba da gudummawa ga halin da muke ciki a yau.
“Allah ka yi rayuwa mai tsawo cikin koshin lafiya farin ciki zaman lafiya da wadata.
Ladan Nasidi.