Take a fresh look at your lifestyle.

Kongo Da Rwanda Sun Gabatar Da Kudirin Samar Da Zaman Lafiya

47

A wani bangare na kokarin da Amurka ke jagoranta na sasanta rikicin Kongo da Rwanda sun gabatar da kudirin samar da zaman lafiya.

Babban mashawarcin shugaba Donald Trump kan Afirka da Gabas ta Tsakiya Massad Boulos ya tabbatar da gabatar da jawabai yana mai bayyana su a matsayin “Muhimmiyar mataki” na samun zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Ana kallon shawarar samar da zaman lafiya a matsayin wata hanya ta budadden saka hannun jari na kasashen yamma a fannin hakar ma’adinai na yankin.

Ministan harkokin wajen Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa “Za a ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe a cikin wannan wata tare da fatan shugabannin kasashen Rwanda da Kongo za su sanya hannu kan yarjejeniyar a tsakiyar watan Yuni a fadar White House, a gaban shugaba Trump da shugabannin kasashen yankin.”

Shawarar samar da zaman lafiya ya biyo bayan taron da aka yi a watan Afrilu a birnin Washington, inda Kongo da Rwanda suka yi alkawarin yin aiki don cimma yarjejeniyar zaman lafiyar karkashin kulawar sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio.

Aisha Yahaya, Lagos

Comments are closed.