Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya matashin Dan Najeriya mai kirkire-kirkire Oluwatobi Oyinlola murnar samun kundin tarihi na Guinness World Record ta hanyar samar da na’urar binciken GPS mafi kankanta a duniya.
Shugaban a tabbataccen adireshin sa @officialABAT a ranar Talatan da ta gabata ya yaba wa Oyinlola bisa hazakarsa ta fasaha tare da bayyana nasarar da aka samu a matsayin wata shaida da ke nuna hazaka da kwazon matasan Najeriya.
“Wani Dan Najeriya, Oluwatobi Oyinlola, ya kirkiro samfurin na’urar bin diddigin GPS mafi ƙanƙanta a duniya mai nauyin 22.93 X 11.92mm tare da damar da ba ta da iyaka don amfani da su a masana’antu daban-daban da kuma fannonin rayuwa” in ji shugaban.
“Ina taya ka murna Oluwatobi kan wannan rawar da ka nuna wa duniya cewa matasan Najeriya za su iya” Ya kara da cewa ya sa hannu tare da PBAT.
Sabuwar na’urar wacce aka gane tare da Rikodin Duniya na Guinness ana tsammanin za a yi amfani da ita sosai a cikin kayan aiki tsaro kiwon lafiya da masana’antar sufuri da ke biyo bayan karamin girmanta da iya daidaitawa.
Hanyoyin kirkire-kirkire na Oyinlola sun hade da karuwar matasan Najeriya da ke samun karbuwa a duniya saboda nasarorin da suke samu a fannin kimiyya da fasaha inda hugaban kasa ya jaddada cewa ci gaban Najeriya ya dogara ne da kirkire-kirkire da kuma kuzarin matasanta.
Aisha.Yahaya. Lagos