Majalisar wakilai ta bukaci a gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar da ta afku a daki ajiye makamai na barikin Giwa da ke jihar Borno tare da mika rahoton ga majalisar domin daukar matakin gaggawa na hana afkuwar lamarin nan gaba.
Majalisar ta kuma yi kira da a gudanar da cikakken nazari kan matakan tsaro a cibiyoyin soja domin hana afkuwar irin wannan lamari da kuma tsara yadda za a karfafa ayyukan tsaro a jihohin Borno da Yobe domin kare jami’an soji da fararen hula.
Kudurin dai ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na Muhimmancin Jama’a na Gaggawa “Game da Rikicin Gobarar Kwanakin baya Makamai a Barikin Giwa da Hare-haren da ake kaiwa Sojoji a Borno da Jihar Yobe” wanda Mista Ahmed Satome ya gabatar.
Da yake jagorantar muhawara kan kudirin Mista Satome ya yi kira ga gwamnati da ta bayar da tallafi da kuma biyan diyya ga iyalan sojojin da lamari ya shafa.
“Wannan gidan mai girma ya lura da tashin gobarar da ta faru a kwanan nan a runduna ta 127 da ke barikin sojoji na Giwa Barracks.
” Sanin cewa ‘yan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare a wasu sansanonin soji a cikin watanni biyun nan Hakanan sani: sojoji da fararen hula da dama ne aka kashe a hare-haren.
“An damu da cewa ‘yan Boko Haram sun kai wa Barack’s hari da yawa kuma matsugunan fararen hula na ci gaba da fuskantar barazana.
“Yawancin hare-haren Boko Haram na baya-bayan nan kan sojoji abu ne mai matukar tayar da hankali, sannan kuma ana gwada jaruntaka da sadaukarwar jami’an sojan mu ta hanyar hare-haren da ake kai wa,” in ji shi.
Da yake bayar da gudunmuwar kudirin, Mista Ahmed Jaha ya yi nuni da cewa matsalar rashin tsaro a Borno na karuwa har ya sa mutane ‘yan gudun hijira Sun karu a Jihar.
A nata bangaren, Misis Zainab Jimba ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta kai dauki ga al’ummar Borno Kuma sauran ‘yan Majalisar Sun bada ta su gudunmawa wajen Gabatar da Kudirin
Majalisar ta yanke shawarar cewa wajabta ne ga kwamitin soja da tsaro na kasa umarnin gudanar da bincike kan lamarin tare da bayar da rahoto cikin makonni hudu (4).
Aisha.Yahaya, Lagos