Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori a wata ganawar sirri da suka yi a fadar gwamnati dake Abuja.
Gwamna Oborevwori ya isa gidan gwamnatin da karfe 3:45 na rana a ranar Talata da ta gabata.
Ganawar ita ce ta farko Oborevwori da shugaban kasar tun bayan sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Idan dai ba a manta ba tsohon Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP Dakta Ifeanyi Okowa da mataimakin gwamna Monday Onyeme da gwamnan jihar Sherrif Oborevwori duk sun koma jam’iyyar APC ne bayan wani babban taron siyasa da aka gudanar a Asaba.
Aisha.Yahaya, Lagos