Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Sanata Aminu Waziri Tambuwal bisa sadaukarwar da yayi wa jihar Sokoto da kasa baki daya a daidai lokacin da dan majalisar ke cika shekaru 60 a duniya.
A cikin sakon taya murna da kakakin shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban kasar ya yabawa jam’iyyar PDP, Sanata bisa ga irin gudunmawar da ya bayar ga tafiyar dimokuradiyyar Najeriya, inda ya tuna da zamansa na shugaban majalisar wakilai daga 2011 zuwa 2015 da kuma wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Sokoto tsakanin 2015 zuwa 2023.
Shugaba Tinubu ya bayyana Sanata Tambuwal a matsayin fitaccen dan siyasa kuma gogaggen lauya wanda aikinsa na jama’a ya nuna jajircewarsa wajen gina kasa da kuma shugabanci nagari.
Ya kuma bayyana jajircewar dan majalisar wajen ciyar da dimokuradiyya gaba da karfafa harkokin mulki a kasar nan.
Shugaban ya yi wa Sanata Tambuwal fatan samun karin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya da kuma samun kyakkyawar makoma ta siyasa domin ya ci gaba da yiwa Najeriya hidima.