Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban ECOWAS Ta Yi Allah Wadai Da Rashin Samar Da Ababen More Rayuwa A Iyakar Seme.

49

Shugaban kungiyar ECOWAS Dakta Omar Touray ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar ababen more rayuwa a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin duk da zuba jari da kungiyar ke yi.

Touray ya bayyana hakan ne a wata ziyarar aiki da ya kai kan iyakar Najeriya da Legas Seme wata mahimmiyar hanyar zirga-zirgar ababen hawa kuma daya daga cikin manyan hanyoyin kasuwanci a yammacin Afirka.

KU KARANTA KUMA: Majalisar ECOWAS na neman sasantawa da jihohin Sahel

ECOWAS ta sake jajircewa kan tsaro, walwala da kuma hadewar tattalin arzikin yankin.

A yayin ziyara shugaban hukumar ta ECOWAS ya tattauna da masu ruwa da tsaki da suka hada da jami’an gwamnatocin Najeriya da Benin kan dabarun inganta hadin kan yankin da kasuwanci da kuma aiwatar da yarjejeniyar ECOWAS mai ‘yanci.

Yayin da yake zantawa da jami’an hukumar kwastam da shige da fice daga Najeriya da Benin shugaban na ECOWAS ya kuma duba yadda ayyukan da hukumar ta samar a ofishin hadin gwiwa.

Ya kuma tabbatar wa gwamnatocin Najeriya da Benin da ma masu ruwa da tsaki kan ci gaba da goyon bayan ECOWAS don ciyar da yankin gaba da kuma kare hakkin al’umma da ke cikin yarjejeniyar ECOWAS na ‘yancin zirga-zirgar mutane da kayyayaki da kuma aiyuka.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.