Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Kasa Tinubu Ya Rantsar Da Kwamishinonin INEC Da Mambobin Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata

722

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.

Kwamishinonin sun yi rantsuwar ne a yayin da aka fara taron majalisar zartarwa na tarayya a ranar a fadar gwamnati da ke Abuja.

Bikin rantsuwar ya biyo bayan jawabin gabatarwar da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Mista Abiodun Oladunjoye ya yi.

Sabbin kwamishinonin INEC su ne Mallam Tukur Abdulrazaq Yusuf mai wakiltar Arewa maso yamma Farfesa Sunday Nwambam Aja mai wakiltar Jihar Ebonyi.

Shugaban ya kuma rantsar da kwamishinoni 2 na Hukumar Kula Da da’ar Ma’aikata (Code of Conduct Bureau) CCB Ikpeme Kenneth Ndem (Jihar Cross River) da Hon. Justice Buba Ibrahim Nyaure Rtd Jihar Taraba.

Wadanda suka halarci zaman majalisar na ranar Litinin sun hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu.

Ministan Kudi da Tattalin Arziki Wale Edun da takwaransa na Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Tattalin Arziki Atiku Bagudu da Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Kasa Mohammed Idris da sauran mambobin majalisar zartarwa.

Taron Majalisar Zartarwa na karshe da aka gudanar a ranar 5 ga watan Mayu ya amince da tsarin tattalin arzikin Najeriya na farko da aka yi niyya don ba da fifiko ga amfani da kayayyaki da ayyuka na cikin gida a duk wasu sayayyar gwamnati.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.