Kimanin masu kada kuri’a miliyan 68 a Philippines ke kan hanyar zuwa rumfunan zabe a zaben tsakiyar wa’adi domin kada kuri’a su. Sama da mukamai na kasa da na kananan hukumomi 18000 ne ake fafatawa a zaben da ke cike da tashen hankula tsakanin daular siyasar Marcos da Duterte masu tasiri.
Daga cikin zabukan da aka fi sa ido a kai har da kujeru 12 da ake fafatawa a majalisar dattawa mai wakilai 24. Sakamakon zai iya zama muhimmi ga shari’ar tsige mataimakin shugaban kasa Sara Duterte saboda majalisar dattawa za ta yi aiki a matsayin alkali a kowace shari’a. Ana bukatar rinjaye kashi biyu bisa uku— kuri’u 16 don yanke hukunci.
Duk da haka a cewar Sanatocin Philippines galibi suna fifita son rai fiye da amincin jam’iyya. “Kowane abin da suke yi a yanzu za su so su tantance inda ra’ayin jama’a yake kafin su yanke shawarar hanyar da za su kada kuri’a lokacin da aka fara shari’ar tsigewar daga baya a wannan shekara.”
Haka kuma a kan zaben akwai ‘yan takarar majalisar wakilai 317 da daruruwan gwamnoni da kantomomi da kuma kansiloli. An bude kada kuri’a ne a duk faɗin Philippines daga 07:00 zuwa 19:00 agogon gida.
Aisha.Yahaya, Lagos