Take a fresh look at your lifestyle.

Firamare: APC Legas Ta kaddamar Da Kwamitin Daukaka Karar Zabe

131

Jam’iyyar APC reshen Jihar Legas ta kaddamar da kwamitin daukaka kara domin sauraron korafe-korafen da aka yi a zaben fidda gwani da aka yi ranar Asabarda ta gabata

Sakataren yada labaran jam’iyyar na jihar Mista Seye Oladejo ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Legas.

Idan dai ba a manta ba a ranar Asabar din da ta gabata ne jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani na shugabanci da kansiloli domin zabar ‘yan takarar da za su fafata a zaben kananan hukumomin Jihar da za a yi a ranar 12 ga watan Yuli.

Zaben fidda gwanin ya fitar da 55 daga cikin 57 da ake sa ran za su yi takarar shugabancin jam’iyyar APC.

Sai dai wasu daga cikin sakamakon zaben da wasu ‘yan takara suka yi watsi da su bisa zargin da aka yi musu wanda ya haifar da zanga-zangar da ‘yan jam’iyyar da suka fusata a wasu kananan hukumomin.

A cewar Oladejo kwamitin na karkashin jagorancin Mista Lawal Pedro SAN babban lauya kuma kwamishinan shari’a na Jihar Legas da kuma Cif Abiodun Olufowobi a matsayin Sakatare.

Ya ce sauran mambobin kwamitin sun hada da Mista Jokotola Pelumi tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Legas Mista Lanre Ogunyemib tsohon Dan majalisar wakilai kuma sakataren jam’iyyar na Jiha da kuma Cif Chukwudi Adiukwu.

“Muna ba da shawara ga wadanda ba su yarda ba da su mika kokensu ga kwamitin nan da karfe 12 na rana ranar Talata 13 ga Mayu 2025″ in ji kakakin APC.

Comments are closed.